23 Disamba 2015 - 12:36
"Sojoji sun yi kuskure kan kisan 'yan Shi'a"

Kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya, Human Rights Watch, ta ce sojojin Najeriya ba su da wata hujjar kashe 'yan Shi'a a Zaria, duk da ikirarin da suka yi cewa mabiya Shi'ar sun yi yunkurin kashe Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai.

A wani rahoto da kungiyar ta fitar ta ce shaidun da ta tattauna da su sun gaya mata cewa sojoji sun kashe 'yan Shia fiye da 300 a kwanakin biyu da suka kwashe suna yi musu luguden wuta.

Human Rights Watch ta ce , "Mun tattauna da shaidu 16 da kuma wasu biyar -- cikinsu har da shugabanni -- wadanda suka gaya mana cewa sojojin Najeriya sun yi ta harbin kan mai-uwa-da-wabi a cibiyoyi uku na 'yan Shi'a a Zaria daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Disamba. Ba zai yiwu a ce tare hanyar da 'yan kungiyar suka yi ya zama hujjar kashe daruruwan mutane ba".

Kungiyar ta kara da cewa, "Sojoji sun kai hare-hare kan cibiyar Hussainniya Baqiyyatullah, da gidan shugaban 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim Al Zakzaky da gidajen makwabtansa da ke Gyellesu da kuma makabartar 'yan Shi'a, Daral-Rahma, a cikin kwanaki biyu. Shaidu sun gaya mana cewa sojojin sun kashe akalla 'yan Shi'a 300 ko fiye da haka.288